1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin badakalar kudi a Afirka ta Kudu

Zahraddeen Lawan/A'RHAugust 26, 2016

Ana tuhumar ministan kudi na Airka ta Kudu da kafa wani sashe a hukumar tattara kudaden haraji na kasar ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/1Jqlp
Südafrika Kapstadt Finanzminister Pravin Gordhan
Hoto: Imago/Gallo Images

Ministan kudi na kasar Afirka ta kudu ya ki amsa gayyatar 'yan sanda, lamarin da ya sa masana shari'a da kwararru ke cewa zargin da ake wa ministan siyasa ce kawai a dai-dai lokacin da kasar ke fuskantar matsalar tattalin arziki. A Cikin wata wasika da hukumar 'yan sandan kasar ta aikewa Pravin Gordhan, ta na tuhumar sa da laifin kafa wani sashe a hukumar tattara kudaden haraji ba bisa ka'ida ba.

Sashin mai kula da manyan laifukan ya kuma ce Gordhan ya karya dokokin aiki na ma'aikatar kudi, inda ya amince da ritayar Ivan Pillay mataimakin babban jami'in tattara haraji na Afirika ta kudu kafin lokacin yin ritayar sa kuma ya dauke shi kwantiragi to sai dai Gordhan ya musanta dukkannin wadannan zarge-zarge.

Ana rade-radinin cewa shugaban kasar Afirika ta kudun Jacob Zuma da wasu na hannun daman sa ne ke son a cire Gordhan saboda tsantsenin sa wajen kashe kudin gwamnati da kuma kin sakin wasu kudaden don samar da nukiliya. Johan Kriegler tsohon joji a kasar ya ce wasu ne a cikin gwamnatin kasar ne ke son yin facaka da kudin al´umma don haka suke kokarin yin amfani da 'yan sanda don cimma wata manufa ta siyasa.

Jacob Zuma Präsident Südafrika
Ana zargin Zuma da kokari wajen ganin an cire Gordhan daga mukaminsaHoto: Getty Images/AFP/M. Safodien

To sai dai a share guda, shugaban Afirka ta Kudu din Jacob Zuma ya fitar da sanarwar cewa ba shi da ikon hana gurfanar da Gordhan, yayin da kuma shugaban babbar jám'iyyar adawa ta DA Mmusi Maimane ya rubutawa majalisar dokoki cewa su gaggauta yin muhawara kan batun Gordhan don kuwa a cewar sa so ake a shafawa Pravin Gordhan kashin kaji.