1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin ACN ga PDP game da zaben 2015

April 8, 2013

Jam'iyar adawa ta ACN a Tarayyar Najeriya ta zargi gwamnatin PDP da yin ruwa da tsaki wajen haddasa rikice rikice a fadin kasar da nufin ci gaba da jan ragamar milkin kasar.

https://p.dw.com/p/18Bp8
Büro der Oppositionspartei "Actopm Congress of Nigeria" in Abuja, Address No. 16, Bissau Street, Wuse Zone 6, Abuja *** Bild von DW-Mitarbeiter Ubale Musa, 28. Januar 2013
Hoto: DW/U. Musa


Babu dai zato kuma ba tsamani jam'iyar adawa ta ACN ta fito ta zargi gwamnatin PDP da kokarin hada rikici a tsakanin musulmi da kirista da kuma Arewa da kudancin kasar da nufin tabbatar da dorewa bisa mulkin kasar a shekara ta 2015. Kakakin jami'yar Lai Muhammed ya ambato wata kwangila ta Naira miliyan dubu biyu da dari hudu da ya ce an baiwa madugun kungiyar OPC Fredrick Feseun da nufin amfani da kudin domin ta da hankali a yankin kudu maso yammacin kasar.Sannan kuma ya kira kame 'ya'yan kungiyar Boko Haram a ginin gwamantin jihar Bayelsa da ke birnin Iko a matsayin wata alamar neman rikici a bangaren PDP duk dai a tunaninsa a cikin burin PDP na hada rikici da nufin dorewa bisa mulki a kasar.

Action Congress of Nigeria ACN
Cibiyar jam'iyar adawa ta ACNHoto: DW/U. Musa


Wannan zargin dai ya ta da hankali a cikin fadar gwamantin kasar ta Aso Rock da kuma ita kanta jam'iyar PDP da kakakin ta Olisah Metu ya kira karyar da bata da tushe da kuma ke da burin jefa al'umar kasar cikin rudani. Shima dai kakakin fadar ta Aso Rock Dr Reuben Abati ya dauki lokaci ya na kare mai gidansa da yace ya ciri tutar zabe mafi inganci a cikin tarihin kasar ta Nijeriya kuma ya ce 'yan adawar kasar na yi masa kazafi ne kawai.
"Ina son baiwa 'yan Najeriya tabbacin shugaban kasar zai ci-gaba a kan kudurinsa na tabbatar da ingantacen zabe kuma babu wani saddabarun 'yan adawa da zai kau da shi daga wannan kuduri."

Sannan kuma Alhaji Lai Muhammed ya yi kazafin cewar an ba da wata kwangilar kare bututun man fetur da nufin samo da wata kafa ta tada hankalin al'umar Arewa maso yammacin kasar. To ina baku tabbacin cewa babu wata kwangila mai kama da wannan daga gwamanti. Sabbin zarge zargen dai na fitowa a dai ai lokacin da kasar ta Najeriya ke kara shiga tsaka mai wuya game da halin tsaro da zaman lafiyar al'umarta, Bisa ga dukkanin alamu na iya kara hargitsa al'amura da ma maid a hannun agogo baya ga kokarin zabukan na shekaru biyu masu zuwa.

Nigerias Präsident Goodluck Jonathan
Shugaban kasar Najeriya Goodluck JonathanHoto: AP


To sai dai kuma a fadar Salihu Lukman dake zaman jigo a jamiyar ta ACN dai zargin nasu na bisa hanya kuma na cike da hujjoji ga duk wani mai hankali cikin kasa. A cikin makon jiya ne dai Faseun din da a baya ya yi kaurin sunan zaman jagora gu kungiyar OPC ta tsagerun Yarabawa ya bayyana aniyar sa ta kafa wata jam'iyyar da ya radawa sunan United Party for Nigeria dake da suna iri daya da ta marigayi Chief Obafemi Owolowo abun kuma da masharhanta ke ta'allakawa da kokari na kawo karshen babakeren ACN din a yankin kudu maso yamacin kasar.

Rahoto cikin sauti na kasa

Mawallafi: Ubale Musa /Issoufou Mamane
Edita :Mouhamadou Auwal Balarabe