1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nageriya: 'Yan kwadogo na neman karin albashi

January 8, 2019

A wani abin da ke zaman kokarin janyo hankali ga masu mulkin tarrayar Najeriya, daruruwan 'yan kwadago sun fara wata zanga-zanga neman tilasta wa gwamnatoci karin albashi a matakan aiki daban-daban.

https://p.dw.com/p/3BCjr
1. Mai-Kundgebung in Abuja
Hoto: DW/Uwais Abubakar Idris

Wasu gungun ma’aikatan a babban birnin tarrayar Najeriya sun gudanar da wata zanga-zangar neman tilasta wa gwamnatin kasar biyan  Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin sabon albashi. An dai tsayiwar gwamin jaki a tsakanin mahukunta na kasar da ke fadin suna biyan 24,00 a matsayin mafi karancin albashin da masu kwadagon da ke fadin ko a biya dubu 30 ko kuma sarki ya ji ba dadi. Babban burin masu kwadagon dai na zaman jan kunne ga gwamnatoci na jihohi dama gwamnatin tarrayar kafin tsunduma a halin yajin aikin a fadar comrade Ayuba Wabba da ke zaman shugaban babbar kungiyar kwadagon NLC kuma jagoran masu zanga-zangar. Daga dukkan alamu zanga-zangar ta samu tagomashi na masu siyasar da ke ganin ba hujjar 'yan mulki na jan kafa ga sabon albashin.