Zanga-zangar ′yan adawa a Tunisiya | Siyasa | DW | 08.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-zangar 'yan adawa a Tunisiya

Ƙasar Tunisiya ta gundura da rashin ci-gaban da ake samu a fannin zamantakewa da tattalin arziƙin kasar.

Dubun dubatan 'yan Tunisiya suka fantsama kan tituna a wannan juma'ar a matsayin wani ɓangare na makokin madugun adawa Shokri Belaid, wanda kisar gillar da aka yi masa ya jefa ƙasar cikin rikicin siyasa. rahotanni sun ce aƙalla mutane dubu 50 suka halarci jana'izarsa duk da ruwan da aka tabka kaman da bakin ƙwarya.

Waɗanda suka gani da ido sun shaida cewa wannan ce janaizar da ta fi yawan mahalarta tun bayan mutuwar marigayi Habib Bourguiba, shugaban ƙasar na farko wanda ya rasu a shekarar 2000. Janaizar wadda aka yi a garinsu dake yankin Jebel al-Jaoud ya cika maƙil da masu zanga-zanga, suna tafe suna faɗin kalaman da ke nuna adawarsu da gwamnati.

Ƙasar Tunisiya wacce ke zaman mafari zanga-zanagr juyin-juya halin da ya kaɗa a ƙasashen larabawa tana fama da rashin jituwa tsakanin masu ra'ayin kishin addini waɗanda ke da rinjaye da kuma 'yan adawa waɗanda ke son ware addini daga harkokin tafiyar da gwamnati, haka nan kuma sun gundura da rashin ci-gaban da ake samu a fanin zamantakewa da tattalin arziƙi tun bayan da aka hamɓarar da mulkin zine al-Abidine Ben Ali a watan Janairun shekara ta 2011.

Soldiers help mourners carry the coffin of slain opposition leader Chokri Belaid during his funeral procession towards the nearby cemetery of El-Jellaz, where he is to be buried, in the Jebel Jelloud district of Tunis February 8, 2013. Tens of thousands of mourners chanted anti-Islamist slogans on Friday at the Tunis funeral of secular opposition leader Belaid, whose assassination has plunged Tunisia deeper into political crisis. REUTERS/Anis Mili (TUNISIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST CRIME LAW)

Jana'izar Chokri Belaid

Wasu masu zanga-zangar sun Allah wadai da Rashid Ghannouchi shugaban jamiyyar Ennahda, 'yan sanda dai sun yi ta jefa hayaƙi mai sanya hawaye domin watsa masu zanga-zangar, ga dai ra'ayin Al-Hadi wani ɗan ƙasar:

"Wannan kisar gillan, kisar gilla ce a kan demokraɗiyya, kisar gilla kan shiƙa-shiƙan matakin farko da ya kamata a bi, da ma kisar gilla a kan kyakyawar fatan 'yan Tunisiya waɗanda suka yi Allah wadai da mulkin kama karya"

Masu zanga-zangar dai sun yi fata Allah ya jiƙan Belaid da rahama amma sun ce su zasu cigaba da gwagwarmayar.

Prime Minista Hamdi Jebali daga jamiyyar masu kishin addini ya ce zai rusa gwamnatin ya kafa wata sabuwa wacce zata ƙunshi ƙwararru su jagoranci ƙasar kafin a yi wani zaɓen.

People attend late opposition leader Chokri Belaid's funeral procession which makes its way to the nearby cemetery of El-Jellaz where Belaid is to be buried on February 8, 2013 in the Djebel Jelloud district, a suburb of Tunis. Thousands of people attend the funeral while Tunis is at a near standstill, with streets deserted, shops shut and public transport at a minimum as a general strike called by a powerful trade union after Bellaid was murdered took effect. AFP PHOTO / FETHI BELAID (Photo credit should read FETHI BELAID/AFP/Getty Images)

Masu zanga-zanga

To sai dai jamiyyarsa ta Ennahda da jamiyyun da ke haɗaka da ita sun ce bai yi shawara da su ba, abunda ke kawo rashin yadda a kan gwamnatin, ya ke muka kawo ruɗani game da makomar siyasar ƙasar. Mohammed Tounsi shi ma wani ɗan Tunisiyan ne wanda ya bayyana ra'ayinsa

"A gani na wannan shawara ce wacce aka yanke cikin gaggawa sakamakon abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, bana tsammanin wannan shawara ce mafi a'ala ga wannan hali da muka sami kanmu, a gani na muddin sahihiyar gwamnatin da aka kafa ta faɗi duk wani gwamnatin da zai biyo baya ma zai faɗi. Fargabar da ake fama da shi ke nan a Tunisiya. Saboda haka abun da akwatunan zaɓe suka kawo dole akwatunan su koma su soke shi."

Tasirin da rikicin siyasar da ma zanga-zanga ke yi kan tattalin arziƙin ƙasar ka iya daɗa yin tsanani a wannan ƙasa wacce bata riga ta tsara kundin tsarin mulki ba wacce kuma ke dogara sosai kan ziyarar masu yawon buɗe idanu.

A yanzu haka dai ƙasar ta tsaya cik, ƙungiyar ƙwadagon ƙasar ta ce a cigaba da yajin aiki, wannan ƙwaƙwarar alama ce mai nuna cewa wannan abun na faruwa ke nan a karo na uku a tarihin ƙasar mai shekaru 70 yanzu. Daga dukkan alamu dai 'yan adawa a Tunisiya ba zasu yarda gwamnati ta yi musu abunda ta ga dama ba kamar yadda Nadia ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ta nunar:

"A duk lokacin da suka kashe wani, zamu ƙara mayar da martani, zamu ƙara yin zanga-zanga, zamu ƙara yin juyin juya hali, ba mune ya kamata mu firgita mu ji tsoro ba, su ne ya kamata su tsorata"

Kawo yanzu babu wanda ya ɗauki alhakin kisan Belaid, lawyer kuma ɗan adawa a jamiyyar da ba ruwanta da addini. Iyalansa sun zargi 'yan jamiyyar Ennahda, zargin da ta ƙaryata, sai dai masu zanga-zanga sun kai hari kan ofisoshin jamiyyar biyu a Tunis da wasu yankuna na tsawon kwanaki biyu yanzu.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin