1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa a Ghana

Jamila Ibrahim/GATJanuary 20, 2016

Kungiyoyin kwadagon kasar ta Ghana sun gudanar da zanga-zangar tasu domin tilasta wa gwamnati da ta janye wani karin haraji da ta yi kan lantarki da ruwan da kuma karin kudin man fetur.

https://p.dw.com/p/1HhLk
Arbeiter demonstrieren in Accra
Hoto: DW/I. Kaledzi

A wannan Laraba ce hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasar Ghana ta gudanarda wata zanga-zangar lumana ta gama gari, domin matsawa gwamnati lamba, a kan bukatar ta yi rangwame akan ababan more rayuwa, bayan tsawon zama akan teburin sasantawa da ta yi da gwamnatin ba tare da samun fahimtar juna ba.

Masu zanga-zangar sun yi ta gudanar da Raye-rayen da wakewa kenan, a lokacin zanga-zangar da ta samu halartar daruruwan mambobin kungiyoyin kwadago da ma’aikatan gwamnati a nan birnin Accra, baya ga na sauran mambobin kungiyoyin da aka gudanar a sauran sassan kasar baki daya. Kungiyoyin kwadagon sun gudanar da zanga-zangar tasu domin kalubalantar gwamnati a kan manyan haraji da ta kirkira da 'yan kwadagon suka kwatanta da kisar gilla, da kuma haurawa na fitar hankali na farashin ababan more rayuwa musamman wutan lantarki da ruwa. Ga dai irin kokawan da wasu jama’a keyi.

Wiederwahl John Mahama in Ghana
Hoto: Reuters

Ra'ayoyin masu zanga-zanga yaki da tsadar rayuwa a Ghana

1"Idan za’a lura sosai, da alamar wannan shugaba namu ba mai daukan shawara ba ne, dan haka lokaci ya yi da ya kamata a nuna masa kwazo kuma wannan shi ne matakin farko. Domin shugaban da zai iya bude bakinsa ya furta cewar duk wanda ya sayi mota ya yi shirin biya haraji ai kenan wannan ba ya san ci gaban al’ummarsa".

2"Karin man fetur din nan ai ba haka yake ba a kasuwar danyen mai ta duniya, dan shi idan kudin zabe ne yake bukata, to su sani fa mu al’ummar Ghana muna cikin halin tasku, kuma za mu yanke wa kanmu shawara"

3"Farashin man fetur ya sauka a kasuwar duniya kuma a bincikawar karshe da na yi yana tsaye ne a kan dala 34 da 'yan kai, amma mu a nan sai haurawa yake ta yi, kuma dama a ce an kara albashinmu ne bayan karin, da ba bu matsala. Harajin yayi yawa".

Hujjojin kungiyoyin kwadagon Ghana na gudanar da zanga-zanga

Kofi Asamoah, babban sakataren hadin guywar kungiyoyin 'yan kasuwa TUC a takaice, wanda ya jagoranci zanga-zangar, ya ce kungiyoyin kwadagon ba za su lamunta ba kuma za su ci gaba da matsa wa gwamnati lamba har sai ta kau da sabon harajin makamashi da ta rattaba, domin dukkan alamu na nunin cewar dokar ita ce ummul haba’isan matsalolin da jama’a suka tsunduma a ciki, inda ya kuma kara da cewar.

"A teburin sasantawar da muka zauna tare da gwamnati sau biyu, babu wata kwakkwarar shawarar da ta gabatar domin mu sasanta, a can dai mun bukaci rangwami ne a kan farashin ababan more rayuwa kuma kwatsam sai ga wannan sabon haraji. Ita dai gwamnati ta ce tana bukatar fadada hanyoyin samun kudaden shiga wanda ba mu yi musun haka ba, amma kuma duk da ikonta na gudanar da ayyukan kasa, da akwai bukatar ta zurfafa tunani kuma ta nemi shawarwari daga dukkan bangarori, kuma da watakila wannan bai cika da ita ba.

Ghanas Präsident John Mahama bei einer Mai-Kundgebung in Accra
Hoto: DW/I. Kaledzi

Zangar-zangar dai ta kasance a cikin lumana ba tare da wasu munanan labarai ba. Gwamnatin dai ta kara farashin ruwa da kaso 67 cikin dari, sai kuma da kaso 59.2 cikin dari a kan lantarki. Kuma duk da cewar kungiyar kwadagon ta bayyana cewar a shirye take ta koma kan teburin sulhun da gwamnati, tun a ranar litinin ne dai ma’aikatar kula da ayyuka da kwadago , a wata ganawa da 'yan jarida ta ce watakila za’a iya samun daidaito ta fuskar farashin ababan more rayuwan, amma a kan batun harajin na makamashi, aikin gama ne wanda ya rigaya ya gama.