Zanga-zangar neman zaman lafiya a Bangui | Labarai | DW | 09.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar neman zaman lafiya a Bangui

Dubun dubatan mazauna babban birnin na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka bazu kan tituna don kira da neman zaman lafiya.

Dubunnan mutane ne suka fito a titunan birnin Bangui na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya duk kuwa da ruwan sama da ke zuba a wannan birni, domin nuna goyon bayansu ga shirin zaman lafiya a wannan kasa da har yanzu ake jiran fitowar sabuwar gwamnatin hadin kan 'yan kasa ta rikon kwarya. Mtanen da suka hada da Musulmai, da Kiristoci, 'yan siyasa da sauran kungiyoyin fararan hulla, sun halarci wannan jerin gwanon sanye da riguna masu kalar fari da bula, da tsanwa da masara da kuma kalar ja ma'ana kalolin tutar kasar ta Afirka ta Tsakiya. Da take magana kan wannan jerin gwano na neman zaman lafiya, Shugabar kasar ta rikon kwarya Catherine Samba Panza, ta nuna matukar farin cikinta. Daga bisani ta yi kira ga masu zanga-zangar da su kama hannu cikin hannu tare da rera wakar adini ta zaman lafiya. Shugabar ta kara da cewa ita "uwa ce mai kaunar illahirin 'ya'yanta, kuma na tatauna da dukkan bangarorin wannan kasa, a kokarin da muke na fitar da sabuwar gwamnati." Sama Panza ta ce ba da dadewa ba za a fitar da sabuwar gwamnati amma kafin nan za a fara da fitar da sabon shugaban gwamnatin.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal