Zanga-zangar neman kawo karshen yajin aikin malaman jami′oi a Najeriya | Siyasa | DW | 26.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-zangar neman kawo karshen yajin aikin malaman jami'oi a Najeriya

'Yan sanda a jihar Kano sun yi taho mu gama da daliban jami'oin da suka gudanar da gangamin adawa da rashin biyan bukatun malamansu.

Daruruwan dalibai ne karkashin inuwar kungiyar dalibai ta kasa a Najjeriya, suka shirya wata zanga zanga a jihar kano, domin nuna takaicinsu na zaman kashe wando da suka shafe watanni suna yi sakamakon yajin aikin gama-gari da malaman jami'oin Najeriya suka shiga, domin tursasa gwamnatin kasar ta cika alkawarin da ta dauka musu a shekarar 2009.

Sai dai zanga-zangar daliban ta gamu da cikas bayan da dakarun 'yan sanda dauke da bindigogi suka hana su yin tattaki zuwa dandalin kwatar 'yanci da ke Silver Jublee a jihar. Lamarin da ya tilastawa daliban kammala zanga-zangar a kofar jami'ar.

©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace

Goodluck Jonathan

Jerin gwanon neman 'yanci a Kano

Daliban, sun shirya yin tattaki ne daga harabar tsohuwar jami'ar Bayero dake Kano, zuwa dandalin Sada Silver Jublee da suke kallonsa a matsayin wani dandalin kwatar 'yanci tamkar dai dandalin Tahrir da ke kasar Masar. To, sai dai fitowarsu ke da wuya sai suka yi kacibis da dandazon 'yan sanda a bakin kofar jami'ar, dauke da bindigogi da kulake, inda suka hana musu rawar gaban hantsin aiwatar da wannan tattaki da suka yi niyya.

Duk wani yunkuri da daliban suka yi na keta shingayen 'yan sandan, abin ya ci tura domin nan da nan 'yan sanda suka gindaya motocinsu a bangarorin da daliban za su wuce, hakan ne ya tilastawa daliban yin katantawa a iya sararin da 'yan sandan suka bari. Sai dai duk da haka, daliban sun ci gaba da rera wakokin neman yanci, tare da ganin baiken matakin da 'yan sandan suka dauka akansu. An dai dauki lokaci ana cacar-baki tsakanin shugabannin daliban da kuma ASP Ahmed Hamza, wanda ya jagoranci tawagar 'yan sandan da suka dakile zanga-zangar.

Die Fotos zeigen protestierende Studenten während ASUU Streik in Kano und anderen Teilen Nigerias. September 2013 zugeliefert von: Umaru Aliyu copyright: DW/Nasiru Salisu Zango

Zanga-zangar dalibai a Kano

Goyon bayan dalibai ga yajin aikin malaman jami'a

Sani Sa'idu Ibrahim, shi ne shugaban kungiyar daliban jami'ar Bayero ta Kano, ya bayyana cewar, fitowarsu dai ta zama wajibi domin dubun dubatar dalibai da ke zaune a gida suna zaman kashe wando, sun dade da kosawa da wannan yajin aiki.

Ya kuma bayyana goyon bayan daliban ga kungiyar ASSU ta malaman jami'a zalla, wadanda yace ko kadan kada su ja baya da batun yajin aiki, har sai gwamnati ta amsa bukatunsu, ya kuma yi kira ga malaman na su da su kira zanga-zanga, wacce za su gabatar kafada da kafada da daliban, domin dai a girgiza gwamnatin kasar.

Daliban dai sun kammala zanga-zanga da kai ziyarar goyon baya ga malaman na su wadanda ke gabatar da wani taron gaggawa dai-dai lokacin da daliban ke gabatar da zanga-zangar. Ibrahim Khalil Abdulsalam shi ne mataimakin shugaban kungiyar malaman jami'a ta ASUU reshen jami'ar Bayero da ke Kano, wanda kuma shi ne ya karbi caffar daliban. Ya bayyana cewar, lokaci ne yayi da dalibai da iyayensu suka gane muhimmancin gwagwarmayar da malaman ke yi. Harma yace za su amsa kiran daliban na shirya gagarumar zanga-zanga, tare da daliban na su.

A karshe dai daliban sun koma cikin harabar jami'ar suna ci gaba da rera wakokin.

Mawallafi : Nasir Salisu Zango
Edita : Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin