Zanga-zangar maluman makaranta a Nijar | Siyasa | DW | 12.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-zangar maluman makaranta a Nijar

Maluman makaranta 'yan kwantaragi a Nijar sun kudiri aniyar ci gaba da yajin aikin game gari tare da zanga-zanga har sai gwamnati ta shafe masu hawaye.

A Jamahuriyar Nijar yau ne aka shiga kwana na biyu na yajin aikin da 'yan ƙungiyar maluman makaranta da ke ƙalƙashin haɗɗaɗiyar ƙungiyar nan ta CPRAS suka tsunduma na tsawon kwani biyar a faɗin ƙasar, a wani mataki na ci gaba da neman haƙƙoƙinsu daga gwamnatin ƙasar.
Tun dai farkon soma karatun boko ne dai 'yan ƙungiyar maluman makaranta,musamman ma 'yan kwantaragi su ke tsunduma cikin yajin aiki wanda akasarin su ke yin su na kwanaki biyu zuwa uku, da zimar neman tanƙwaso
gwamnati ta biya musu buƙatunsu wanda tun tuni a cewar maluman aka riga aka rattaba hannu a kan su. Sai gashi far an fara samun matsin lamba daga maluman masu yajin aiki inda suka fara yajin aiki na sati guda, kuma ma a wannan karon yajin aikin ya zo ne a daidai lokacin da
maluman ke kokawa da rashin samun albashin su na watan Fabrairu da ya gabata.

Mohamed Yatane shine Sakataren ƙungiyar maluman makaranta ta CYNACEB reshen Jihar Tahoua,ya ce:Sai mu ga kamar niya ce babu wajan gwamnati sabili da a daidai
wannan lokaci da nake magana, maluman makaranta basu samu albashin watan da ya gabata ba, kaga kenan abun baƙin ciki ne kuma babban abun baƙin cikin shine akwai wasu malumai 'yan kontragi sabin ɗauka da suke biyar
Gwamnati watanni uku da ba'a biya su ba.
Wannan yajin aikin ya fi illa ne a cikin karkara ganin cewa harma wanda a da suke zama basa bin yajin aikin suka baro dajin da zimmar shigowa birni, domin neman albashin su da yayi wuyar fitowa, sannan kuma a wani labari da yake yawo ta wayoyin salula tsakanin maluman ana ganin bisa dukkan alamu Gwamnati tafi mayar da hankalinta ne ga yaƙin dake gudana a kasar Mali, inda ma ake batun wasu kuɗaɗe na
CFA Miliyan dubu saba'in da gwamnatin ta zuba cikin yaƙin na Mali, alhali su maluman suna buƙatar aƙalla Miliyan dubu biyar ne domin magance matsalolin karatun da yaƙi ci ya ƙi cinyewa.Issoufou Sherif na ɗaya daga cikin maluman makaranta na cikin karkara kuma memba a ƙungiyar CPRAS.
Yace : Irin matsalolin dake dakwai na yajin aiki a cikin karkara kana ganin dukkan makarantu an rufe su sabili da abun da bai taka kara ya taka ba sabili da abun da ya kamata a sa ɗan gyaran wannan matsaloli bai da yawa idan akayi la'akari da abun da gwamnati take zubawa kan yaƙin ƙasar Mali, domin mun ji an ce aƙalla a zuma CFA Miliyan dubu
Saba'in, kan wannan yaƙi alhali mu muna bukatar aƙalla Miliyan dubu biyar.
Sai dai wannan yajin aikin yazo ne ya tarda wata matsala da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a fuskar tafiyar karatu a nan Tahoua tsakanin maluman makaranta na sakandre da hukumomin ilimi tun bayan fitar da wasu ɗallibai biyu da akayi daga cikin wasu makarantu masu zaman kansu sakamakon rishin ladabi, inda kuma bayan wata tantannawa hukumomin

School in Central African Republic

jihar ta Tahoua suka buƙaci da a sake baiwa wannan yara wata dama abun da su maluman suka ce ya saba ma dokar ilimi.
Na nemi jin ta bakin Abdurahamane Ango Daraktan Ilimi mai zurfi na jihar Tahoua inda yake cewa…
Yace : Har yanzu mu dai ƙofofin mu a buɗe su ke zamuci gaba da tattanawa domin idan ana tattanawa komai zai walwale, a fannin wannan shekara ta karatu bamu da falgaba domin su malumai wanda na ke jinjina musu suna ƙoƙari sosai domin da zaran ance an shirya to aikin da suke a dan ƙanƙanin lokaci mai yawa ne domin ko a shekarar bara mun
samu irin haka amma sakamakon da muka samu a nan jihar Tahoua yafi na ko'ina.
Saidai har kawo yanzu bisa dukkan alamu, babu wata magana mai daɗi da ta shigo kunnuwan maluman masu yajin akin , inda suka ce su suna bukatar ne ko da ma Gwamnati ta ce bata da halin biyan buƙatunsu a wannan lokaci to tayi musu magana mai daɗi ta hanyar ɗaukan wani sabon
alƙawali mai gamsarwa amma kawai sai shiru kake ji kamar an shuka dussa.

Mawallafi: Salisou Boukari
Edita: Yahouza Sadissou Madobi


Sauti da bidiyo akan labarin