1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zanga-zangar kisan wani bakar fata a Amirka

May 30, 2020

Zanga-zanga na ci gaba da barkewa a Amirka yayin da batun kisan mutumin nan bakar fata George Floyd  ke ci gaba da daukar sabon salo.

https://p.dw.com/p/3d0nZ
USA Atlanta | CNN | Tod George Floyd durch Polizeigewalt in Minneapolis | Protest
Hoto: Reuters/D. Chambers

Ana zargin dan sanda farar fata mai suna Derek Chauvin da danne wuyan mutumin bakar fatar gami da shake ma sa wuya har na tsawon mintuna tara, lamarin da ake zargin ya yi sanadiyyar mutuwar George Floyd.


Duk da a ranar Jumma'a an shigar da karar dan sandan a gaban kotu ana zarginsa da kisan kai, amma masu zanga-zanga a biranen Amirka irinsu New York da Los Angeles da Atlanta da kuma Washington na ci gaba da fitowa kan tituna don nuna rashin amincewarsu. 

''Ina ba duk wani bakar fata mazaunin Amirka shawara da ya rinka duba bayansa idan yana tafiya, kada ku yi wasa da 'yan sandan nan domin suna ganin kamar sun fi karfin doka, ya zama wajibi mu rinka tafiya muna waigen bayanmu domin watakila kai ne mutum na gaba da za a yi wa irin wannan.'' inji wata matashiya bakar fata a wurin zanga-zanga a Amirka.