Zanga-zangar kin jini gwamnati a Koriya ta Kudu | Labarai | DW | 05.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar kin jini gwamnati a Koriya ta Kudu

Hukumomi a Koriya ta Kudu sun baza dubban 'yan sanda a kan tituna gabannin wata zanga-zanga ta 'yan adawar da ke bukatar shugabar kasar Park Geun-Hye ta yi marabus a game da zargin cin hanci.

Shugabar ta rika yin hawaye tare da yin nadama a game da abin da ya faru  wanda ta amince ta tafka kuskure tare da cewar a shirye take kotu ta saurareta a lokacin da take yin jawabin.Shugaba Park dai ta amince da bada goyon baya ga wata aminiyarta  babbar jami'ar gwamnati wacce aka kama bayan da ta yi amfani da mukaminta wajen tilasta wa wasu kamfanonin kasar zuba kudade ga wasu cibiyoyin na bogi  wanda daga bisani ta karkata kudin zuwa ga asusunta na ajiyar kudadenta.