Zanga-zangar goyon bayan gwamnatin Tunisiya | Labarai | DW | 04.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar goyon bayan gwamnatin Tunisiya

Dubbannin 'yan Tunisiya sun gudanar da boren nuna goyon bayan kawancen jam'iyyun da ke mulki a Tunisiya.

Dubun dubatan 'yan kasar Tunisiya ne suka gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansu ga gwamnatin kawancen kasar a karkashin jam'iyyar masu kishin addini, a wani abin da ke zama bore mafi girma tun bayan juyin juya halin kasar a shekara ta 2011. Magoya bayan jam'iyyar Ennahda, wadda ke da matsakaicin ra'ayin addini, sun bukaci jama'a ne su fito su nuna goyon bayansu ga gwamnati, domin kalubalantar masu boren da ke neman rusa gwamnati, wadanda suka yi ta jerin gwano a kwanakin baya bayannan.Tun da farko dai, a wannan Asabar ce, fira ministan kasar ta Tunisiya, Ali Larayedh, ya yi kira ga kwantar da zaman lafiya daga bangarorin masu boren nuna goyon baya da kuma masu adawa da gwamnatin, wadanda su ma suka shirya gudanar da ta su zanga-zangar a karshen makon.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman