Zanga-zangar adawa da wariyar launin fata na karuwa
June 3, 2020A yayin da zanga-zanga ke ci gaba a wasu jihohin Amirka bayan kisan wani bakar fata George Floyd da wani Dan sanda farar fata yayi, wasu gwamnatocin kasashen duniya son soki matakin da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta dauka a kokarin shawo kan rikicin.
Chaina da ta sha suka da matakan ladabtarwa daga Amirkan ta hanyar aza mata takunkumi bisa zargin tauye hakkin dan adam, na daga cikin kasashen da suka soki matakin amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga-zanga adawa da wariyar launin fata, kasar Iran da ita ma ta dandan kudarta a hannun Amirka, a nata bangaren ta yi tsokaci, inda ta yi amfani da ire-iren kalaman Shugaba Trump ga al'ummar Iran a yayin duk wata zanga-zanga na cewa duniya ta ji kukansu kuma tana tare dasu.
Afrika ta Kudu ita ma ta shawarci gwamnatin Amurka da ta sassauta matakan da ta ke dauka kan masu boren, hakazalika Firaiministan Britaniyya Boris Johnson da Shugaban darikar Katolika Fafaroma Francis.Yanzu haka akwai kasashen duniya da jama'a ke gudanar da zanga-zangar lumana don adawa da wariyar launin fata.