Zanga-zangar adawa da Nicolas Maduro | Labarai | DW | 02.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar adawa da Nicolas Maduro

Masu adawa da mulkin Shugaba Nicolas Maduro na kasar Venezuwela sun ce za su cigaba da yin zanga-zanga don yin matsin lamba ga shugaban har sai ya sauka daga mulki.

'Yan adawa suka ce mutanen da suka haura miliyan guda da suka fantsama kan tituna a jiya na son ganin an yi kuri'ar raba gardama kan batun saukar Shugaba Maduro daga gadon mulki. Galibin masu wannan zanga-zanga dai sun ce sun dawo daga rakiyar gwamnatin kasar ce saboda yadda ta gaza magance matsalar karanci abinci da magunguna sakamakon matsalar da tattalin arzikin kasar ke fuskanta a halin yanzu.

To sai dai a share guda masu goyon bayan gwamnatin kasar su ma sun gudanar da tasu zanga-zangar a jiya musamman a Caracass babban birnin kasar inda suka ta rera kalaman Allah wadai da masu adawa da gwamnatin wanda suka ce suna so ne kawai su dagula lamura a kasar.