1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar adawa da gwamnati a Iraqi

March 8, 2013

'Yan Iraqi mabiya tafarkin sunni na ci gaba da shirya gangami a kudancin kasar da ma Bagdada don nuna adawarsu da mulkin nuna wariya da gwamnatin Maliki ke nuna mu su.

https://p.dw.com/p/17u00
Hoto: Reuters

A gangamin da suka yi wa take da "Dama ta karshe" da suke ba wa gwamnatin Maliki da ta dau matakan gyaran da suka yi watanni uku suna hankoran ganin ta aiwatar, da kuma sakin wadanda ake tsare da su kan dalilan siyasa da na tsaro. Masu zanga zangar sun yi kashedin kara iza wutar yin bore cikin lumana don ganin bayan gwamnati Maliki muddin ta ci gaba da yin kunnen uwar shegu da bukatunsu; suna masu musanta zargin da gwamnati ke yi musu na rera taken nuna bambanci akida.

"Shin ba tare muka yi ta dandana kudarmu da takunkumin da kakaba mana ba? So nawa za a harbi dan sunni dan shi, a ya zo ya cece shi? so nawa dan shi'a ke yin shahada a fada da muke da azzalimai? Sai dan sunni ya dauki makaminsa ya ci gaba da fafatawa, Allah ne ya hada mu tare, kuma korin gwarakanmu da gwamnati ke yi ba zai yi nasara ba."

Irak Baquba Anti-Regierungs Demo
IHoto: Reuters

A nasa bangaren firaminista Nuri al Maliki wanda shi mabiyin tafarkin shi'a ne, ya gargadi jagororin shirya gangamin da su guji rura wutar nuna banbanci, da aikata abin da zai kai ga wargaza kasar;

"Ya ku jagororin shirya wannan gangami,da ku masu zanga zanga, idan har ku ka ba da kofa a masu daga taken bangaranci da banbancin akida,da wadanda ke ba da kudi don afuta zanga zanga, to kasar nan za ta tsunduma cikin yakin basasa,ba ku hankalta da abin dake aukuwa a makwabtanku ba, shin ku na son mu shiga cikin halin kara zube da yakar junar da ba wanda ya san karshensa?"

Watanni uku a jere kenan ,mazauna yankunan kudancin na Iraqi su ka yi ta shirya zanga zangar neman kawo sauye sauyen siyasa a kasar. Ita dai zanga zangar da ta kara kamari bayan da wata kotu a kasar ta Iraqi ta yankewa mataimakin shugaban kasa,Tariqil Hashimi hukuncin kisa, bisa zarginsa da hannu wajen daukar nauyin dana bama baman da ya addabi kasar,kamar yadda kafa kahon zukar da gwamnatin ta maliki da ta yi wa ministan kudin kasar,Al Aisawi wanda shi ma dan sunni ne, har ma daga baya ya yi murabus,na daga cikin dalilan da ya sanya ake cewa lalle biri ya yi kama da mutum.

Irak FallujaAnti-Regierungs Demo
Hoto: Reuters

"Akwai wadanda ke cewa wannan zanga zangar ta siyasa ko ta nuna banbanci ce. Sam ba haka abin yake ba. 'yan kasa ne da suka gaji da mulkin danniya suke neman kwatar wa kan su hakkokinsu."

Ko da a kwanakin baya,sai da matashin shehin shi'a nan Muktada al Sadar da ke da gagarimin tagomashio a kasar,ya fito fili ya ce,yana tare da bukatun masu zanga zangar ta tabbatar da mulki gaskiya da adalci batare da nuna wariya ba.

Irak Bagdad Anti-Regierungs Demo
Hoto: Reuters

Ita dai Iraqi ta na sahun kasashen da aka sanya a matakin farko cikin kasashen larabawa wajen handama da sama da fadin da jami'an gwamnati ke yi da kudin talakawa, kuma ake iko a cikinta tsakanin jagororin addinai da na kabilu. Masharhanta na hasashen cewa talakawa za su jagoranci juyin juya halin a cikinta don kawo karshen mulkin kashe mu raba da jagororin siyasa da na kabilun kasar ke yi.

Rahoto cikin sauti na kasa

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe