Afirka ta Kudu na fuskantar zanga-zanga
October 14, 2015Talla
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da fuskantar fushin al'umma sakamakon halin tabarbarewar tattalin arziki da kasar ke kara shiga. Kungiyar ma'aikatan sarrafa karafa ta kasar "NUMSA" da ke zaman babbar jagorar adawa da jam'iyyar Shugaba Jacob Zuma ta ANC a Afirka ta Kudu ce ke jagorantar zanga-zangar. Masu zanga-zangar dai na dauke da tutoci da ke dauke da rubutu kamar haka: "A yi waje da gwamnatin Zuma" da kuma wani rubutun da ke cewa: "Masu almundahana na karbar haraji daga wajen talakawa".