Zanga-zangar adawa a Kwango | Siyasa | DW | 12.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-zangar adawa a Kwango

Jami'an 'yan sanda a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar nuna adawa da sabuwar dokar zabe a gaban majalisar dokokin kasar.

Manyan jam'iyyun adawar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwangon ne dai suka kira gagarumar zanga-zangar da akallah mutane 300 suka halarta, a dai-dai lokacin da 'yan majalisar dokokin kasar ke shirin fara tabka muhawara a kan sabuwar dokar zaben. 'Yan adawar dai na da'awar cewa sabuwar dokar za ta sharewa Shugaba Joseph Kabila na Kwangon fagen yin tazarce ne idan wa'adin mulkinsa ya kare a shekara ta 2016 mai zuwa.

Amfani da sakamakon kidaya wajen yin zabe

Shugaba Joseph Kabila

Shugaba Joseph Kabila

Gwamnatin Kabila dai na son yin amfani da sakamakon kidayar jama'a da za a gudanar a wannan shekara ta 2015 da muke ciki, wajen yin zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki da ya kamata a gudanar a shekara ta 2016 maizuwa, wanda kuma a cewar masu fashin baki da 'yan adawa hakan ka iya baiwa gwamnatin damar ci gaba da zama kan karagar mulki har na tsahon shekaru biyu.

Cikin wani yanayi na hargitsi ne dai aka buda zaman taron majalisar dokokin wadda aka sa ran za ta dukufa ne wajen yin muhawara a kan sabuwar dokar zaben da gwamnati ta mika gabanta, sai dai kuma wasu daga cikin 'yan majalisun na bangaren adawa sun shigo zauren majalisar ne dauke da busa, inda duk tsawon lokacin da aka dauka wajen gabatar da dokar suka yi ta busa tare da rera wakoki, sai dai hakan bai karyawa mukaddashin ministan cikin gidan kasar Evariste Bishab gwiwa ba wajen gabatar da dokar.

Amfani da hayaki mai sa hawaye

Gangamin kungiyar 'yan tawaye ta M-23

Gangamin kungiyar 'yan tawaye ta M-23

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar harba musu barkonon tsohuwa, wanda hakan ya tilasata masu neman mafaka a ofisoshin jam'iyyun adawar da ke makwabtaka da ginin majalisar. Kuduru Kasango shi ne tsohon kakakin shugaba Kabila da a halin yanzu ya koma bangaren adawa kuma yana daga cikin masu wannan zanga-zanga ya kuma ce ba za su gudu ba domin suna da 'yancin tsayawa a harabar ginin jam'iyyar adawa ta UNC. A nasa bangare shugaban gungun 'yan majalisu na jam'iyyar PPRD mai mulki a Jamhuriyar Dimokaradiyyar ta Kwango Ramazani Shadari ya sanar da cewa wannan doka ta kawo sababbin canje-canje da suka hada da batun kawar da ban-banci tsakanin jinsi.

Shidai Shugaba Joseph Kabila da ke zaman tsohon soja ya samu damar darewa kan karagar mulki ne yana da shekaru 29 a duniya cikin watan Janairun shekara ta 2001 bayan da aka yiwa babansa Laurent Kabila kisan Gilla. Kuma bayan yakin basasa a kasar da ya kawo karshe a shekara ta 2003, an gudanar da zaben farko a shekara ta 2006 a karkashin jagorancin shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin