1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ekwado: Tarwatsa masu bore da zanga-zanga

Abdoulaye Mamane Amadou
October 9, 2019

Jami'an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa dandazon masu zanga-zanaga da suka kudri anniyar mamaye harabar majalisar dokokin a kasar Ekwado.

https://p.dw.com/p/3QvSh
Ecuador Proteste in Quito
Hoto: Reuters/I. Alvarado

Arangama ta barke tsakanin jami'an tsaron Ekwado da masu bore da zanga-zangar nuna fushi kan karin kudin farashin man fetir, biyo bayan sun samu kutsawa a cikin harabar majalisar na wani dan lokaci.

Wannan lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da dubban jama'a ke shirin fitowa gudanar da wata gagarumar zanga-zanga domin karba kiran kungiyoyin kwadago da suka yi fatali da hauhawar farashin man fetir.

Bore da zanga-zangar al'umma da ke ci gaba da dumi na kara ta'azzara harkokin yau da kullum da ma tabarbar da aikin hakar man fetur din kasar Ekwado.