Zanga-zanga a Sao Paulo
June 9, 2014Talla
Masu aiko da rahotannin sun ce mtasan sun datse hanyoyi da shingaye a tsakiyar birnin inda suka cina wuta ga kondaye na shara da kuma tayoyi, tare da kawo cikas ga al'amuran zirga- zirga. Yayin da ya rage kwanaki uku a soma gudanar da gasar cin kofin duniya na ƙwalon ƙafa a Brazil.
Har yazuwa yanzu an gaza cimma daidaito tsakanin gwamnatin da ƙungiyoyin ƙwadago na sufurin jiragen ƙasa da motocin bus da ke yin yajin aiki a Saulo Paulo inda nan ne za a buɗe wasannin ran Alhamis mai zuwa.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman