Zanga-zanga a Masar | Labarai | DW | 01.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Masar

Dubban masu goyan bayan Mohammad Mursi sun shirya zanga-zanga a birane daban-daban.

Dubun-dubatar jama'a a garurruwa daban-daban na ƙasar Masar sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga shuga Mohammed Mursi.Masu aiko da rahotanin sun ce masu gangamin sun riƙa sukar 'yan adawa cewar, inda suna adawa da kudurin to su bari a je zaɓe a ga mai ƙarfi.

Hakan kuwa na faruwa ne a sa'ilin da ƙungiyoyin 'yan adawa ke ci gaba da yin gangami a dandalin Tahrir, inda suka kwashe kwanaki suna yin bore na ƙin jinin ƙarin ƙarfin ikon da shugaban ya baiwa kansa,sannan kuma da matakin da majalisar tsara mulkin ƙasar ta ɗauka na yin hamzari wajan kammala dokokin tsarin mulki na ƙasar a daftarin da majalisar wacce 'yan uwa musulumi ke da rinjaye a kai, ta amince da shi,wanda shugaba Mursi zai sa hannu kan daftarin ƙudirin a nan gaba, bayan ya karɓe shi kafin a gudanar da zaɓen raba gardama a kai cikin kwanaki 15 masu zuwa.

Mawallafi: Abdourahaman Hassane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi