Zanga-zanga a Kwango | Siyasa | DW | 23.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-zanga a Kwango

Daruruwan mutane suka fito a birnin Beni da ke yankin gabashin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango domin zanga-zangar nuna adawa da rundunar wanzar da zaman lafiya

Daruruwan mutane sun yi zanga-zangar nuna adawa da rundunar wanzar da zaman lafiyar Majalisar Dinkin Duniya ta MONUSCO, suna zarginsu da rashin tabuka komai wajen yaki da kungiyar 'yan tawaye na ADF. Shaidun gani da ido dai sun ce, masu zanga-zangar sun yi kakagida ne a farfajiyar ofishin majalisar suna kona tayoyi, suna kira da a janye dakarun daga kasar.

Su dai dakarun wanzar da zaman lafiyar, masu hulan kwano mai ruwan bula da yanayin ya kasance haka, sun yi ta harbi ta sama don tarwatsa masu zanga-zanga, da wannan bore da suka fito suna yi, mazauna birnin na Beni suna nuna fushinsu ne game da wasu matasa biyu da dakarun na MONUSCO da na Kwangon suka harbe har lahira.

Bisa bayanan masu rajin kare hakkin bil adama a yankin, matasan biyu na daga cikin wasu matasa ne da suka yi dammara da adduna da mashi da duwatsu, suka kai wata farmaki wa tawagan dakarun da niyyar kawar da su, daga baya kuma suka gamu da ajalinsu a sanadiyyar wutar bindigan da dakaruin suka harba domin tsira da rayukansu.

Daga cikin ayyukan MONUSCO a wannan yanki har da kare al'ummar daga hare-haren da suke samu a-kai-akai daga kungiyoyin tawaye masu yawan gaske. Tun watan Yuli ake batun kwance dammarar kungiyar tawayen ADF, kuma fushin al'ummar ta kara ruruwa ne sakamakon wani hari mai munin gaske da kungiyar ta kai a 'yan makonnin da suka gabata, wanda ya hallaka mutane akalla 80.

To sai dai kungiyar ta MONUSCO ta bakin kakakinta Charles Bambara lokacin wata hira da ya yi da tashar DW, ta bayyana cewa takaddamar da bincike bayan rasuwar matasan biyu yanzu kuma tana jiran sakamakon ne.

Dangane da zanga-zangar ranar larabar, mai magana da yawun MONUSCOn ba ya so ya ji komai, a maimakon haka, kungiyar na cigaba da kwantar da hankalin al'umma, tana neman hadin kansu, inda ta ke cewa tana aiki tukuru wajen kwance dammarar kungiyar ta ADF kamar yadda mataimakin kwamandan rundunar Jean Baillaud ya bayyana wa jama'ar na Beni mahimmancin hadin kai da aiki tare.

Sai dai duk da haka, rundunar ta MONUSCO ta rasa kimarta a idanun mazauna wannan yanki, suna matukar tsoron 'yan kungiyar ADF, wadanda ake kyautata zaton suna da mayaka 400 ko a ranar juma'ar da ta gabata sai da suka kashe mutane 20 a wani kauye da gatari da adda bisa bayyana wadanda suka tsallaka rijiya da baya.

Sauti da bidiyo akan labarin