Zanga-zanga a kusa da ofishin jakadancin Amirka da ke Beirut | Labarai | DW | 02.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a kusa da ofishin jakadancin Amirka da ke Beirut

Al'ummar kasar Lebanon da Falasdinawa na zanga-zanga a kusa da ofishin jakadancin Amirka da ke kasar Lebanon, inda suke bayyana kyamar shirin gwamnatin Amirka na kawo karshen rikicin Isra'ila da Falasdinawa.

Tun da farko masu zanga-zangar dauke da tutocin Falasdinu sun yi jerin gwano a Arewa maso Gabashin birnin Beirut suna sukar lamirin Amirka duk da irin matakin tsaron da mahukunta suka dauka don tsaron ofishin jakadancin na Amirka.

A ranar Asabar dai ne jagoran Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi barazanar yanke hulda da kasashen Isra'ila da Amirka yayin da yake jawabi a taron shugabannin kasashen Larabawa, bayan ministocin kasashen wajen kasashen na Larabawa sun zargi Amirka da yunkurin mayar da hannun agogo baya a samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.