1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana nuna kin jinin China a Hong Kong

July 1, 2019

An gudanar da gagarumar zanga-zanga a tsibirin Hong Kong domin kin jinin China

https://p.dw.com/p/3LQRP
Hongkong China Protest Parlament Polizei
Hoto: Reuters/T. Siu


Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin China a tsibirin Hong Kong sun fantsama cikin majalisar Dokoki a wannan rana ta Litinin bayan sun rusa shinge da 'yan sanda suka sanya a mashigar majalisar. Masu zanga-zangar na dauke da tutar Birtaniya tun ta lokacin mulkin mallaka domin tuni da zagayowar ranar da aka mika tsibirin na Hong Kong ga China shakaru 22 da suka gabata. 

Masu aiko da rahotanni na cewa dubban al'ummar sun yi kaca-kaca da maduban silke na majalisar bayan shafe tsawon lokaci na zaman durshin a gurin kafin su kai ga shiga ciki inda suka cicire duk wasu hotunan 'yan majalisar.
'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa su amma hakan ta ci tura duba da yawan masu zanga-zangar. Sai dai daga bisani boren ya rikide ya zuwa zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar wacce ta dauki wani sabon kudiri na mika masu laifuka ga China kafin daga bisani ta yi watsi da kudirin da haifar da cece-kuce a tsibirin na Hong Kong dake karkashin China.