Zanga-zanga a Hong Kong | Labarai | DW | 09.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Hong Kong

An yi wata taho mu gama tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga a Hong Kong lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutane da dama.

Masu boren dai sun yi fito na fito da jami'an tsaron ne don nuna rashin amincewarsu da matakin da hukumomi a kasar suka dauka na hana sayar da abinci a kan tituna.

'Yan sanda dai sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma yin harbi a iska don tarwatsa masu zanga-zangar daidai lokacin da suke jifansu da kwalabe da duwatsu.

Masu aiko da rahotanni sun ce an lalata motocin 'yan sanda da gine-gine a yankin Kowloon inda wannan lamari ya wakana, wanda ke zaman mafi muni da aka gani tun bayan da aka yi zanga-zanga ta neman girka dimokradiyya a kasar shekaru biyun da suka gabata.