1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a Cuba

July 13, 2021

Shugaban kasar Cuba na zargin Amirkawan Cuba da amfani da kafafen sada zumunta na zamani wajen shirya zanga-zangar da aka gudanar a ranar Lahadin data gabata.

https://p.dw.com/p/3wP3f
Proteste in Kuba
Hoto: Alexandre Meneghini/Reuters

Jami'an 'yan sanda a Cuba sun fantsama kan tituna a daidai lokacin da shugaban kasar ke wannan zargin ga zanga-zangar da aka gudanar a ranar Lahadi saboda tashin gwauron zabi da kayayyaki suke yi a kasuwanni da kuma karancin abinci.

Zanga-zangar da aka gudanar a yawancin biranen kasar dai na daga cikin nuna adawa ga tsaurara matakai da ake gani cikin shekaru, baya ga batun annobar corona a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ya fada cikin wani mayuwacin hali saboda takunkumin da kasar Amirka ta sanyawa kasar. Tuni dai dama mahukunta suka baiyana aniyar dakatar da zanga-zanga yayin da kawo yanzu aka kama gomman wadanda suka gudanar da ita.