Zanga-zanga a Chicago | Labarai | DW | 28.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Chicago

Dubban jama'a sun yi gangamin domin nuna damuwa a kan rashin zartas da hukunci a kan wani dan sanda da ya kashe wani matashi baƙar fata

Masu yin gangamin waɗanda suka datse tituna da shingaye sun riƙa hana jama'a shiga shaguna domin yin sayaya.Kisan wanda ɗan sandar ya aikata a kan matashin yau kusan shekara guda, duk da cewar akwai shedu na aikata kisan da gangan har yanzu sharia ta faskara. Wannan matar na a cikin masu yin zanga-zangar

''Ga shedun bidiyion fa na kisan da aka yi kusan watannin tara amma har yanzu ba yi sharia ba akwai wariya a ake nunawa tsakanin farar fata da bakaken fata a Amirka.''