Zanga-zanga a Afirka ta Kudu | Labarai | DW | 12.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Afirka ta Kudu

Dubban jama'a a birnin Pretoria na Afirka ta Kudu sun pantsama a kan tituna, a zanga-zangar da 'yan adawar suka kira domin tilasta wa shugaba Jacob Zuma da ya yi marabus daga kan karagar mulki.

Hakan kuwa na zuwa ne gabannin zaman majalisar dokokin kasar wacce za ta ka'da kuri'ar yanka kauna ga shugaban kasar.Shugaba Jacob Zuma wanda ake zargi da laifin cin hancin na fuskantar bore a 'yan kwanakin baya-baya nan, tun bayan da ya yi wa majalisar ministocinsa gyaran fuska wadda a ciki ya salami minitan kudin kasar Pravin Gordhan.