Zamfara: Ta′azzarar harin barayin shanu a kauyuka | Siyasa | DW | 16.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zamfara: Ta'azzarar harin barayin shanu a kauyuka

Munin hare-haren barayin shanu a kauyukan Zamfara ya haddasa asarar rayuka da kwararar daruruwan ‘yan gudun hijira zuwa babban birnin jihar wato Gusau.

A Najeriya yayin da hukumomin kasar ke gwagwarmayar murkushe
kungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin kasar, a jihar
Zamfara da makwabtanta da ke Arewa maso Yammaci, barayin Shanu na cigaba da cin karensu babu babbaka. Kananan yara da mata wadanda suka cika sansanin ‘yan gudun hijirar da ke Gusau,sun tsere ne bayan barayin sun kashe iyayensu da mazajensu da ‘ya'yansu.

Kusan a kullum rana sai barayin sun afka ma wani Kauye, sun hallaka makiyaya tare da sace shanunsu. Shugaban Miyatti Allah na jihar Zamfara Alhaji Tukur Jangebe ya sheda cewar, sun tura motoci a dauko gawarwaki da wasu mutanen da aka raunata a harin da aka kai a wannan Litinin, ya na mai cewar bai san iyakar mutanensu da barayin shanun suka kashe ba a wannan dan tsakani.‘Yan gudun hijirar kimanin 300 ne yanzu haka a sansanin da ke
Gusau. Sai dai kuma saboda ana ci gaba da kawo wasu. A yanzu haka
shugaban hukumar ‘yan gudun hijira ta jihar Zamfara Injiniya Sunusi
Muhammad Kwatarkwashi ya ce, ba za su kididdige yawansu ba da kuma bayar da alkaluman mutanen da aka kashe.

Manazarta lamurra dai na cigaba da cece-kuce kan yadda gwamnatin
Tarayyar Nijeriya ke sako-sako da hare-haren na barayin shanu. A
ganinsu, a irin yadda take daukar matakai na yaki da ‘yan Boko Haram, idan da za a maida kai cikin kankanin lokaci ana iya kawo karshen wannan matsala da a yanzu ta addabi yankin Arewa maso Yammacin kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin