1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zamfara: Mace-mace a harin 'yan bindiga

Mouhamadou Awal Balarabe
March 30, 2018

 Wasu 'yan bindiga sun kashe akalla makiyaya 36 a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso yammacin Nijeriya a wani hari da hukumomi suka dangantaka da na ta'addanci.

https://p.dw.com/p/2vFWX
Frauen mit Ziegen in Zentral-Niger (Zinder)
Hoto: DW/Larwana Hami

Kakakin 'yan sandan jihar Muhammad Shehu ne ya yi wannan sanarwa a Gusau, inda ya danganta farmakin da aka kai kauyen Bawon-Daji da hari na barayin shanu. Dama dai a jiya Alhamis gwamnati ta bayyana cewar mutane 15 ne wannan hari ya ritsa da rayukansu baya ga wadanda suka samu rauni.

Wani basaraken jihar zamfara ya bayyana wa manema labaru cewa jami'an tsaro na ci gaba da bincike don gano wasu gawawwaki. Idan za a iya tunawa dai tu shekaru biyun da suka gabata ne gwamnatin ta tura da sojoji  jihar Zamfara, bayan da sace-sacen mutane don neman kudin fansa da kuma fashi da makami da satar dabobbi suka fara zama ruwan dare a jihar.  A watan Fabirairun da ya gabata ma, sai dan mutane 18 zuwa 41 suka rigamu gidan gaskiya bayan da 'yan bindiga suka bude wuta kan' yan kasuwa da mazauna garin Birane na Zamfara.