Zaman makoki na kwanaki uku a kasar Cote d′Ivoire | Labarai | DW | 14.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman makoki na kwanaki uku a kasar Cote d'Ivoire

Mahukuntan kasar sun kuma dauki karin tsauraran matakan tsaro tare da girke dakaru cikin shirin ko ta-kwana a wurare daban-daban na fadin kasar baki daya.

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku kana ya daga shirin kasar na yaki da ta'addanci zuwa matsayi na kololuwa bayan hare-haren ta'addancin da aka kai wasu wurare shakatawa da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21. A wannan Litinin ministan tsaron cikin gida Hamed Bakyoko ya rage yawan wadanda suka mutun daga mutum 22 zuwa 21 biyo bayan hare-haren da aka kai kan otel-otel guda uku a ranar Lahadi. Hare-haren sun auku ne a yankin Grand-Bassam mai tazarar kilomita 40 kudu da gabashin birnin Abidjan cibiyar kasuwancin kasar. Ministan ya ce daga cikin wadanda suka mutu akwai fararen hula 15 'yan kasar da kuma baki da sojoji uku sai kuma 'yan bindiga uku. Yanzu haka dai kasar ta dauki karin tsaurara matakan tsaro tare da girke dakaru a cikin shirin ko ta-kwawna, sannan ta fadada wuraren tsaro a kusa da ofisoshin jakadanci, makarantu da wuraren taruwar jama'a. Kungiyar al-Kaida reshen yankin Magreb ta dauki alhakin kai hare-haren.