Zaman makoki a Somaliya bayan harin bam | Labarai | DW | 15.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman makoki a Somaliya bayan harin bam

Harin bam da aka kai a tsakiyar birnin Mogadishu ya kasance mafi muni a tarihin kasar a cewar 'yan Somaliya, inda Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku.

Somalia Mogadischu Bombenanschlag (Reuters/F. Omar)

Harin bam da aka kai a tsakiyar birnin Mogadishu na ran 14 ga watan Octoba 2017

Shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed da ake kira da sunan Farmajo, ya kai ziyara a babban asibitin Erdogan da ke birnin na Mogadishu inda aka kwantar da wadanda harin bam din ya rutsa da su. Ko ma da yake ya zuwa yanzu babu wani adadi da hukumomin kasar suka bayar na yawan wadanda suka mutu a harin, amma kuma wani adadi na wucin da kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP ya bayar na cewa mutane akalla 40 sun mutu yayin da wasu sama da 100.

Babban asibitin Erdogan ya tabbatar da karbar mutane 205 da suka samu raunuka cikinsu kuwa sama da 100 na cikin mawuyacin hali. 'Yan kasar ta Somaliya dai sun ce wannan hari shi ne mafi muni da aka kai a tarihin kasar, inda wata babbar mota shake da bama-bamai ta tarwatse a kofar wani Otal da ke tsakiyar birnin Mogadishu, kuma wuri ne da ke da cinkoson jama'a. Sai dai har yanzu babu wani ko wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin. 'Yan kungiyar Al-Shabaab masu alaka da Al-Qaida na yawan kai hare-haren kunar bakin wake a birnin na Mogadishu da kewaye.