Zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra′ila | Labarai | DW | 18.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra'ila

Shugabannin Falasdinu za su jefa ku'riar tantance komawa ga zaman sulhu da Isra'ila, ba tare da sharadi ba.

Wani jami'in hukumar Falasdinu ya sanar da cewar a wannan Alhamis (18. 07. 13) ce jagororin Falasdinu za su jefa kuri'a a kan daftarin shirin samar da zaman lafiya tare da Isra'ila, wanda kasar Amirka ta tsara, amma kuma ba tare da gindaya sharadin da ya shafi batun yankunan da ita Isra'ilar ke ci gaba da mamaya ba. Jami'in ya ce abin da ya fi muhimmanci dangane da daftarin da sakataren kula da harkokin wajen Amirka John Kerry ya tsara, shi ne sake komawa ga tattaunawar, amma ba tare da dakatar wa ko kuma hana ci gaba da samar da matsugunai a yankunan Yahudawa'yan kama-wuri-zauna ba. Ya kara da cewar, daftarin na Kerry, ya kuma tanadi cewar, idan har Isra'ila ta ci gaba da gina sabbin matsugunai a dai dai lokacin da tattaunawar ke ci gaba da gudana, to, kuwa, su ma Falasdinawa za su iya sake gabatar da bukatarsu ta shiga cikin kungiyoyin kasa da kasa, inda kuma za su nemi daukar matakin shari'a a kan gwamnatin isra'ilar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu