Zaman lafiya a Mali na tangal-tangal
May 12, 2015Talla
An dai kai harin kwantar bawnanne kan wata kombar motocin soji da ke kan yanya, kusa da birnin Timbuktu, yankin da sojojin Faransa da na MDD suke da sansani. Harin ya zo ne 'yan kwanaki gabanin yarjejeniyar zaman lafiya da MDD ke yunkurin samarwa ta tabbata, a ranar Jumma'a mai zuwa. Tun a watan da ta gabata ne dai, ake samun arangama tsakanin sojojin gwamnatin Mali da 'yan tawayen Abzinawa.