Zaman kotu kan yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar | Siyasa | DW | 23.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaman kotu kan yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Mutane da dama sun gurfana a kotu wadanda ake tuhuma da yunkurin juyin mulki ga gwamnatin Shugaba Issoufou Mahamadou ta Jamhuriyar Nijar.

A Jamhuriyar Nijar bayan dakatar da zaman shari'ar wasu manyan hafsoshin kasar da aka tuhuma da lafin yunkurin juyin mulki a yau ne wata kotun hukunta laifukan soja ke sake dawowa game da batun don ci gaba da yin shari'ar. Fiye da mutane 12 ne ketun ke tuhuma da aikata laifin na son hambarar da gwamnati ciki har da wani Janar din soja Salou Soulaimane da ke a matsayin dan uwa ga tsohon shugaban gwamnatin rikon kwarya ta mulkin soja Janar Salou Djibo.

An dai shafe tsawon lokaci ana ta kai ruwa rana da takkadama mai zafin gaske tsakanin tarin lauyoyin da ke kare habsoshin sojoji 12 da ake zargi da yunkurin na juyin mulkin inda zaman kotun na musamman da ke hukunta laifukan soja ke zargi da aikata zagon kasa da cin amanar kasa

Tun daga farko lauyoyin sun kalubalanci manbobin kotun hudu bisa abinda suka kira rashin cancanta ganin cewar daya daga cikin manbobinta na da mukamin Janar fiye da na sauran manbobin lamarin da kuma ya kai ga Alkali mai sharia zare daya daga cikin alkalan a dan lokaci tare da mare gurbinsa da wani mai mukamin Canal.

Kana lauyoyin sun kuma kalubalanci sahihancin kotun ita da kanta suna masu cewar tsarin kotun da kundin hukunta laifukan sojoji da take dogaro da shi sun saba kundin tsarin mulki.

Sauti da bidiyo akan labarin