Zaman dar-dar yayin zaben shugaban Guinea
October 11, 2015A wannan Lahadin ne ake gudanar da zaben shugaban kasa a Guinea Conakry a cikin wani hali na fargabar barkewar tashin hankali tsakanin magoya bayan gwamnati da kuma na adawa. Mutane bakwai ne dai suka rasa rayukansu a ranar Jumma'a da ta gabata yayin tashin hankali da ya barke tsakanin magoya bayan Shugaba Alpha Conde da kuma na madugun 'yan adawa Dalein Diallo.
Shida daga cikin 'yan takara bakwai sun nemi a dage zaben, lamarin da gwamnatin ta ce ba zai yiwu ba. Suna zargin gwamnati da gaza yin sahihiyar rejistar masu zabe da kuma raba katunan zaben yadda ya kamata.
Shugaba Alpha Conde na neman wa'adin mulki na biyu. Ya dare kan kujerar mulki ne a shekara ta 2010 bayan da kasar ta Guinea Conakry ta shafe shekaru da dama karkashin mulkin kama karya na sojoji. Mutane miliyan shida daga cikin al'umma miliyan 12 da kasar ta kunsa ne suka cancanci kada kuri'a