Zaman dar-dar a arewacin Mali | Labarai | DW | 13.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaman dar-dar a arewacin Mali

Mazauna Kidal na arewacin Mali sun bayyana fargabar sake tsunduma cikin yaki.

Jami'ai a garin Kidal da ke arewacin kasar Mali sun bayyana damuwarsu akan komawar mayaka - masu tsattsauran ra'ayin addini zuwa yankn, inda mazauna yankin kuma suka bayyana ganin 'yan tawayen Abzinawa dauke da makamai, lamarin da suka ce ya sabawa yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a cikin watan Yuni, wanda kuma ke kara janyo zaman dar-dar ga matsalar tsaro a yankin. Wadannan rahotannin na zuwa ne a dai dai lokacin da shugabannin mayakan da ke neman 'yantar da yankin Azawad suka bayyana shirinsu na mikawa hukumomi ragamar kula da ofisoshin gwamnan yankin, da kuma tashar rediyon Kidal da suka fada hannun 'yan tawayen da ke da ala'ka da kungiyar al-qa'ida bayan juyin mulkin watan Maris na shekara ta 2012 a kasar. Ko da shike Faransa ta yi nasarar jagorantar 'yantar da arewacin kasar a farko farkon wannan shekarar, amma har yanzu garin Kidal na cikin rudani, inda hatta a farko farkon wannan watan ma aka kashe wasu 'yan jaridun Faransa biyu a garin na Kidal yayin da suke yin wata hira.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu