Zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar Faransa
May 6, 2012Jama'a na kaɗa ƙuria'a a zaɓen shugaban ƙasa a Faransa a zagaye na biyu wanda ake fafatawa tsakanin shugaba mai barin gado Nicolas Sarkozy da Francois Hollande jagoran jam'iyyar yan gurguzu. Tuni dai aka bu
ɗe runfuna zaɓe wanda ake sa ran cewa mutane kusan miliyion 46 zasu jeffa ƙuria'a."Wani wanda ya ɗada kuria'a sa kennan , ya na mai cewar suna fatan duk wanda ya sami nasara a zai duba bukatun al 'umma"A wani hasahen da ka baiyana a ranar juma'a da ta gabata ya nuna cewar jagoran jam'iyyar ta socilaiste zai zarta abokin hamayar sa da yawan ƙuri'u. A zagayen farko dai na zaɓen Hollande ya samu sama da kashi 28 cikin dari na ƙuria'a da aka ka kaɗa yayin da fitaccen shugaban ke da kashi 27.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh