Zagaye na biyu a zaben mahukuntan Bangui | Siyasa | DW | 08.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zagaye na biyu a zaben mahukuntan Bangui

Za a je zagaye na biyun tsakanin Anicet Georges Dologuele da kuma Faustin Archange Touadera wadanda dukkaninsu sun taba rikon mukamin Firaminista a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Zentralafrikanische Republik - Anicet Georges Doleguele

Georges Dologuélé dan takarar da ke kann gaba a zaben Bangui

Sakamkon wucan gadi na zaben da hukumar zaben mai zaman kanta ta wallafa a ranar Alhamis ya nunar da cewa Anicet Geroges Dologuele na jamIyyar URCA shi ne a sahun gaba da kashi 23,78 cikin dari a yayin da Faustin Archange Touadera dan takara mai zaman kansa ya samu kashi 19,42 cikin dari na kuri'un da 'yan kasar suka kada a zaben da ya wakana a ranar 30 ga watan Disambar da ya gabata. Idan dai har a nan gaba kotun tsarin milkin kasar ta tabbatar da wannan sakamako to kuwa wadannan 'yan takara biyu wadanda ko wanansu ya taba rikon mukamin firaminista a kasar tasa za su fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar na ranar 31 ga wannan wata na Janairu.

Afrika Wahlen in Zentralafrika

Masu zabe a Bangui

Tuni dai ko wane daga cikin wadannan 'yan takara biyu ya fara daukar matakan zawarcin kuri'un 'yan kasar tasa da nufin lashe zaben a zagayen na biyu. Anicet Dologuele dan takarar da ya zo na farko a zagayen farko na zaben ya bayyana burinsa ga al'ummar kasar tasa yana mai cewa:

"Ina neman mulki ne dan 'yan Afirka ta Tsakiya mazansu da matansu su miliyan biyar da rabi da ke da fatan samun makoma mai kyau. Kuma dan haka nake kira garesu da su dage su bani goyan baya fiye da yadda suka ba ni a zagayen farko domin ni kadai ne dan takarar da ya samu kuri'u a ko wane yanki na kasar nan kuma ina ganin wannan ba karamar yarda da amana ba ne suka nuna min ,dan haka ni kuma zan yi duk abin da ya dace domin nuna masu cewa na cancanci samun wannan yarda da suka ba ni"

To sai dai daga nasa bangare Faustin Archange Touadera dan takara mai zaman kansa yana ganin shi ne mutuman da ya dace da bukatun 'yan jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na wannan lokaci:

Zentralafrikanische Republik Wahl - Sicherheit in Bangui

Jami'an tsaro na sanya idanu a Bangui

"Ya ce na ga cikin wata irin himma da azama 'yan kasar nan suka fito suka yi zabe ranar 30 ga watan Disemba,wannan abu ne mai mahimmancin gaske kuma na nuni da cewa suna fatan ganin sun fita daga cikin wannan mawuyacin hali da suke ciki dama samun zaman lafiya.Dan haka za su dage domin zabar shugabannin da suka amince da su.Kuma na yi farin cikin da 'yan kasata wadanda da dama suka zabe ni da bani yarda ta la'akari da manufofin da na gabatar masu"

.A ranar Litanin da ta gabata kashi biyu daga cikin uku na 'yan takara 30 da suka fafata a zaben shugaban kasar sun nuna rashin amincewarsu da yanda zaben ya gudana har ma suka bukaci da a dakatar da kidayar kuri'un zaben.Amma a bisa matsin lambar gwamnatin rikon kwarya da ma kasashen duniya masu gardamar suka mazaya banda Karim Meckassoua dan takarar da aka yi zaton ka iya lashe zaben amma ya kare a matsayin na bakwai wanda ya lashi takobin kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotun tsarin milki.

Sauti da bidiyo akan labarin