1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabukan shugaban kasa a Mali da Zimbabwe

August 2, 2013

Jaridun Jamus sun maida hankalin su ga zabukan da aka gudanar cikin wannan mako a kasashen Mali da Zimbabwe.

https://p.dw.com/p/19Itc
Hoto: imago stock&people

A game da kasar Zimbabwe,  jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace an dai yi zabe, amma  a lokacinsa, al'ummar Zimbabwe da dama basu sami damar kada kuri'unsu ba, yayin da tun ma kafin a kammala kidaya kuri'u, jam'iyar shugaban kasa mai ci ta Robert Mugabe, wato Zanu-PF tace ita ce ta lashe zaben. A kasar dai ranar Laraba aka yi zaben shugaban kasa da na yan majalisar dokoki, inda  aka maida hankali kan yadda zaben zai kaya tsakanin shugaban kasa mai ci da kuma abokin takararsa,  Morgen Tsavangira na jam'iyar adawa ta MDC. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace  tun ma kafin a kammala kada kuri'u, yan kallo na cikin gida  da na ketare da suka lura da zaben suka nuna shakkarsu a game da yadda yake gudana. Shima shugaban jam'iyar adawa Tsvangirai ya kwatanta zaben a matsayin  cuta da kuma cin amanar kasa, yayin da Robert Mugabe, shugaba mai ci ya kwatanta shi a matsayin ra'ayi da bukatun yan Zimbabwe.

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung ta duba zaben shugaban kasa ne da aka yi a kasar Mali. Tace zaben ya gudana ba tare da tashin hankali ba, kuma  yan kallo da suka lura da zaben sun yaba da yadda aka yi shi. Jaridar tace hakan ya bada mamaki ganin cewar Mali a baya-bayan nan bata komai sai shiga kanun labarai saboda tashin hankali da rikicin yan tawaye, amma sai gashi zaben ya gudana lami-lafiya. Barazanar  kungiyar nan ta yan tawaye mai suna Mujao da tace zata daddasa nakiyoyi a runfunan zabe  bai tabbata gaskiya ba, saboda a zaben na ranar Lahadin da ta wuce, babu inda aka sami wani rahoto na aukuwar rtashin hankali ko fashewar bom, duk kuwa da dimbin jama'a da suka fita domin  kada kuri'unsu.

Jaridar  Neue Zürcher Zeitung  a nata sharhin ita ma tyi yabo ne da yadda zaben  Mali aka yi lami lafiya ba tare da wani tashin hankali ko hatsaniya ba. Hakan, inji jaridar  ya faranta ran shugabanni a birin Bamako da Paris, musamman ganin cewar a farkon wannan shekara ne kasar ta Mali ta kama hanyar rushewa, inda sai da Faransa ta tura sojojinta 400 suka hadu da takwarorinsu na Afirka domin tabbatar da zaman lafiya da fatattakar an tawaye da suka mamaye mafi yawan arewacin kasar. Sai dai kuma inji jaridar, duk gwamnatin da za'a kafa a Mali, zata kasance tana da gagarumin aiki a gabanta na gyaran kasa da sake hadin kan kasa da kuma kawar da sauran abin da ya rage na yan tawayen Abzinawa, wadanda har ya zuwa tsakiyar watan Yuli suka mamaye yankin Kidal a arewacinta.

Mali Präsidentschaftswahl 30./31. Juli
Kampe na zaben shugaban kasa a MaliHoto: DW/K.Gänsler

Manufofin taimakon raya kasa da basu da amfani, wadanke ke ci gaba da tilastawa kasashen Afika su kasance masu dogaro da karbar tamako. Wannan dai shine  yadda jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara sharhinta a game da taimakon raya kasa da kasashe masu arziki suka saba baiwa kasashen Afrika. Jaridar tace me Afrika ta samu daga taimakon raya  kasa na tsawon shekaru hamsin? Me al'ummar nahiyar Afka suka  amfana daga taimakon miliyoyi dubbai da aka rika turawa zuwa nahiyar Afirka a tsawon wananan lokaci daga ketare? Ko da shike ana sane da cewar  abubuwa yan kalilan ne suka hade nahiyar Afika wuri guda, amma matsalolin kasashen yankin, musamman na kudu da hamadar Sahara  duk iri daya ne. Jaridr tce irin wannan sadakata da ake baiwa Afrika ba zai kawo karshen talaucin dake addabar nahiyar ba.

Daga cikin wadanda suka fi sukan manufofin bada taimakon raya kasa ga kasashen Afrika, har akwai sanannen marubucin adabin nan, Wole Soyinka  na Najeriya da ya taba samun lambar Nobel a fannin adabi da dan jaridar Uganda Andrew Mwenda da masanin tatalin arziki dan kasar Ghana da George Ayittey. Wadanan masana suka ce basa son ganin Afika taci gaba da  kasancewa mai mika kokonta na bara a ko wane lokaci, yayin da kasashe masu arziki suke ci gaba da nuna sha'awar ganin nahiar taci gaba a matsayin nahiyar da bata iya taimakon kanta da kanta.

Mali Geberkonferenz in Brüssel
Taro a Brussels na nemarwa Mali kudin taimakon raya kasaHoto: Georges Gobet/AFP/Getty Images

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Yahouza Sadisou