1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A cigaba da kashe Zabiya a Malawi

Zulaiha Abubakar
June 28, 2018

Zabiya a Malawi na fuskantar kisan gilla sakamakon rashin daukar matakan tsare rayukan su daga bangaren mahukunta kamar yadda kungiyar kare hakkin bil'Adama ta kasa da kasa Amnesty International ta sanar a yau Alhamis.

https://p.dw.com/p/30Thi
Mosambik Albinos in Quelimane
Hoto: DW/M. Mueia

Wani bincike na baya-bayan nan da hukumar ta fitar ya bayyana adadin zabiyan da aka yi wa yankan rago a kasar ta Malawi zuwa 21 tun daga shekara ta 2014 zuwa yanzu, da niyyar amfani da gabobin jikin su don yi arzikin dare daya kamar yadda wasu daga cikin al'ummar kasar suka camfa. Da take karin haske kan rohoton Daraktan kungiyar kare hakkin bil'Adama ta kasa da kasa mai kula da shiyyar kudancin Afirka Deprose Muchena tayi kira ga kasashen da ke makotaka da Malawi, a kan su dauki ingantattun matakan tsaro don hana safarar zabiya ko kuma gabobin jikinsu ,ta kuma kara da cewar a halin yanzu kasashen Afirka ta Kudu da Muzambik da kuma Swaziland sune sahun gaba wajen sayen gabobin Zabiya a Duniya.