Zabiya na fuskantar kisa a Tanzaniya | Zamantakewa | DW | 18.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Zabiya na fuskantar kisa a Tanzaniya

'Yan sanda a Tanzaniya na tsare da wasu matsafa kusan ɗari biyu a yankin arewacin ƙasar waɗanda ake zargi da yin farautar zabiya,waɗanda suke kashwesu domin yin tsafi.

Hassan Khamisi zabiya ne wanda ke da kimanin shekaru 17 da haifuwa wanda ke zaune a ƙauyen Shinyanga da ke a arewacin Tanzaniyar yana zuwa makaranta kamar sauran yara . A hirar da DW ta yi da shi ya ce har kullum yana cikin tsoro da fargaba.

''Wannan al'amarin ya cusa mani tsoro a ryuwata;har ma lokacin da na ke ganin ina da tabbas,da barcina da tashina duk ina cikin tsoro,saboda waɗannan mutane koi'na suna nan, ko da shi ke ma makarantarmu na da cikakken tsaro amma dai duk da haka bai isa ba.''

Ƙungiyoyi masu fafutuka sun dage wajen kare lafiyar Zabiyan

Albinos dai kamar yadda ake kiransu ko zabiya wani ciwo ne na jini da ke zaman daliln rikeɗerwa launin fata ta yi jajir har ma ta gaza jure wa rana. Wanda matsafan suka canfasu cewar suna yin tasiri sossai wajen yin asiri domin samun gallaba a kan al'amura na rayuwar.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a cikin watannin shidda na baya-baya nan zabiyan na fuskantar barazana ta kisa ko jikkatawa a cikin ƙasashen Tanzaniya da Malawi da kuma Burundi. A Tanzaniyar dai tun daga shekarun 2000 kawo yanzu sama da zabiya 72 aka kashe waɗanda suka haɗa da yara ƙanana har ma da jarirai waɗanda akasari a kan tsintsi gwawarkinsu bayan an cire wasu sassa na jikinsu.

Mnazarta dai na hasashen cewar farautar ta zabiya ta ƙara tsananta ne a cikin watannin shida na baya-baya nan a Tanzaniyar saboda zaɓuɓɓukan na gama gari da ake shirin yi a ƙasar a ckin watan Oktoban da ke tafe,abin da ake ganin wasu da dama daga cikin 'yan siyasar ke neman ɗauki na matsafan ta hanyar shidabaru.

Sama da zabiya 15 a ka kashe a Tanzaniya a cikin wannan shekarar

A ƙasar dai ta Tanzaniya an ƙaddamar da wani kampe na yaƙi da lamarin na kisan zabiya wanda ake yi wa laƙabi da sunan Imetosha watau ya isa. Saboda daƙile abin da ƙungiyoyin masu fafutuka suka kira na kwashe dogon lokaci da aka yi ana kallon lamarin ba tare da yin hukuncin ba.Abdlla Possi masannin shari'a a jami'ar da ke a Tanzaniya shi ne lauya na farko da ke fafutukar kare zabiyan:

''Dukkanin ƙungiyoyin da ke fafutukar neman hakkin zabiya yakamata su gane abu ɗaya shi ne cewar hannu guda ba ya iya wanke jiki, dolle sai an haɗu domin gama ƙarfi guri guda saboda Tanzaniya babbar ƙasa ce domin tinkarar matsalar.''

A tsakiyar watan Janairu da ya gabata ne dai gamnatin ƙasar Tanzaniya ta zartas da dokar hana aiyyukan tsafi a ƙasar domin kawo ƙarshen matsalar ta kisan zabiya. Kafin a farkon watan Maris shugaba Jakaya Kikwete ya ƙudiri aniyar ɗaukar matakin kare zabiya, wanda matsafan ke sayan sassan jikin kowane domin aikin tsafin dalla Amirka 600.