Zaben ′yan majalisun dokoki a Italiya | Labarai | DW | 04.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben 'yan majalisun dokoki a Italiya

A wannan Lahadi 'yan kasar Italiya kimanin milyan 46 ke zaben 'yan majalisun dokoki a wani zabe mai cike da rashin tabbas kan wanda zai samu rinjaye a tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna.

Tun dai da misalin karfe bakwai ne agogon kasar aka buda runfunan zabe, inda za a zabi 'yan majalisar wakilai 630 da kuma na dattawa 315. Batun 'yan gudun hijira da na tsaro da kuma sake farfado da tattalin arzikin kasar ta italiya na daga cikin abubuwan da ka iya yin tasiri a zaben.

Daya daga cikin tsofin 'yan siyasar kasar na jamiyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya kuma tsohon Firaminista Silvio Berlusconi, na sa ran jam'iyyarsa ta samu nasara tare da abokin kawancansa Antonio Tajani, wanda ya zaba a matsayin wanda zai zama rike mukamun firaminista idan har suka yi nasara a zaben. Sai dai ana ganin akwai wuya jam'iyya guda ta samu kai adadin da ake so na kashi 40 zuwa 45 cikin 100 na yawan kuri'un kafin samun rinjaye a majalisar bisa sabon tsarin kudin zaben kasar.