1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magoya bayan 'yan adawa za su fito kada kur'a a zaben Mali

Abdoulaye Mamane Amadou
March 28, 2020

Babbar jam'iyyar adawa a Mali ta yi kira ga jama'ar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu su kada kuri'a a zaben 'yan majalisun dokokin da za a yi a kasar ranar Lahadi.

https://p.dw.com/p/3aAR9
Parlamentswahl in Mali
Hoto: DW/K. Gänsler

Jam'iyyar adwa a Mali ta bukaci magoya bayanta da su fito kada kuri'a a zaben 'yan majalisun dokokin kasar duk da yin garkuwa da ake da madugun 'yan adawar kasar Soumaila Cisse.

Sai dai a daidai lokacin da jam'iyyar adawar ke kira ga magoya bayanta da su fito kada kuri'a, wasu da dama daga cikin jam'iyyun adawar kasar sun bukaci da a dage zaben duba da yadda matsalar cutar cCoronavirus ta soma samun gindin zama a kasar, inda ya zuwa yanzu aka tabbatar da samun kalla mutun 18 dauke da ita.

Har ya zuwa yanzu dai ba a ji duriyar madugun 'yan adawar kasar Soumaila Cisse ba, wanda wasu 'yan bindiga suka kai wa ayarinsa farmaki tare da yin garkuwa da shi a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa garin Niafunke da ke yankin Tounbouctou na arewacin kasar don gudanar da gangaminsa na yakin neman zabe.