Zaben ′yan majalisa a kasar Guinea Bissau | Siyasa | DW | 09.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben 'yan majalisa a kasar Guinea Bissau

A ranar Lahadi ake zaben 'yan majalisar dokoki a kasar Guinea Bissau inda jam'iyyu 21 za su fafata a neman kujeru 102.

Bayan kwashe kimanin shekaru uku ana tata burza game da siyasar kasar ta Guinea Bissau da Portugal ta yi wa mulkin mallaka kafin 'yanci a 1974 za a iya cewa kasar ta kama hanyar warware matsalar da ta hana komai tafiya. Matakin kuma da zai bude kofar ci gaba da gudanawar al'amura tsakanin kasa da kasa a cewar Gabriel Dava jami'in diflomasiya kuma jagoran shirin Raya kasa na Majalisar Dinkin Duniya UNDP.

Tun daga watan Agusta na shekarar 2015 kasar ta uku a arzikin Cashew a Afirka ta fada rudani na siyasa bayan da Shugaba José Mário Vaz, ya sauke firaministan a wancan lokaci wato Domingos Simões Pereira, sai dai wadanda suka biyo bayansa sun gaza wajen samun rinjaye na goyon baya a majalisa. Cikin jam'iyyu 21 da ke neman wakilici a majalisar dokokin kasar dai na gaba su ne jam'iyyar ta PAIGC da PRS da hadakar "Madem G15" ana ganin su za su wawashe kujerun. Sai dai a fadar Domingos Simões Pereirashugaban masu rinjaye na jam'iyyar ta PAIGC da ta taka rawa a zaben 2014 ya ce sun sake dinkewa da aniya ta sake samun rinjaye a kujerun majalisar a wannan karo ma.

Shekaru hudu da tsayar lamura dai a Guinea Bissau ya haifar da rufewar makarantu da jami'oi tsawon shekaru, fannin aikin shari'a ya tsaya ga fannin lafiya. Shi kansa wannan zabe dai na ranar Lahadi da dama jam'iyyun da ake gani na barin kudi kudade ne da suka samu daga kungiyoyin tallafi na kasa da kasa da ke fatan ganin 'yan kasar ta Guinea -Bissau sun dau alhaki da ya rataya a wuyansu wajen samar da sauyin al'amura kasarsu a yi tafiya da kowa bayan zabe da zai haifar da gwamnati.

Sauti da bidiyo akan labarin