1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Austriya na zaben 'yan majalisa

Zainab Mohammed Abubakar
September 29, 2019

Jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya a karkashin jagorancin Sebastian Kurz mai shekaru 33 da haihuwa ne ake saran za ta samu gagarumar nasara

https://p.dw.com/p/3QQrB
Österreich Wahlen Wahlkampf Zv Debatte
Hoto: Reuters/L. Foeger

Hasashen manazartan lamuran siyasa na nuni da cewar, jam'iyyarsa ta al'umma na shirin samun kashi 33 daga cikin 100 na kuri'un da ake kadawa, kana ta masu sassaucin ra'ayi da masu ra'ayin gurguzu ke faffutukar neman matsayi na biyu.

Tun da misalin karfe biyar na safiyar yau ne dai aka bude rumfunan zabe a wannan kasa da ke da mutane wajen miliyan 6.4 da suka cancanci kada kuri'a.

Zaben da za'a kammala da misalin karfe uku agogon GMT, inda lokacin ne kuma ake saran fara sanar da sakamakom farko.