Zaben Siri Lanka ya zama abin koyi | Labarai | DW | 09.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben Siri Lanka ya zama abin koyi

Shugaba Barack Obama na Amirka ya bayyana farin cikinsa kan yadda kasar Siri Lanka ta kammala zabenta cikin yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sri Lanka Präsidentschaftswahlen Maithripala Sirisena 9.1.2015

Maithripala Sirisena sabon zababben shugaban Siri Lanka

Shugaba Obama ya bayyana shugaba mai barin gado Mahinda Rajapakse na Siri Lanka da nuna dattaku wajen mika mulki cikin nutsuwa, inda ya ce nasarar da kasar ta sako ne ga duk kasar da ke da muradin ganin girkuwar Demokaradiya.

Bayan da Obaman ya tayashi murna, zababben shugaban mai shirin hawa mulki Maithripala Sirisena ya bayyana fatan cika alkawuran da ya daukar wa al'ummar kasar:

"Mutane miliyan shida da dubu 200 sun dora mana alhakin kasarmu ta haihuwa da al'ummarta, saboda haka ina tabbatar wa al'umma cewa na dauki wannan alhaki don ganin na cimma bukatar abinda wadanda suka zabemu suka bukata".