Zaben shugaban kasar Gini-Bissau | Labarai | DW | 18.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasar Gini-Bissau

Masu zabe na can na kada kuri'a a zaben shugaban kasa zagaye na biyu, inda 'yan takara biyu ke fafatawa domin kafa iko a kasar da ta yi fama da juye-juyen mulkin soji.

Manyan 'yan takara biyu da suka fi samun kuri'a yayin zaben watan jiya su ne Jose Mario Vaz da Gomes Nabiam ke fafatawa a zaben. Tsohon ministan kudi kasar Jose Mario Vaz kuma dan takaran jam'iyya mai mulki ya zo na farko, yayin zaben da ya gabata da fiye da kashi 40 cikin 100. Shi kuwa Nuno Gomes Nabiam ya zama na biyu da kashi 25 cikin 100. Duk wanda ya samu nasara yana da aiki na raba sojojin kasar ta Gini-Bissau da harkokin siyasa wanda suka mamaye tun lokacin da kasar ta samu 'yanci.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman