Zaben shugaban kasar Cote d′Ivoire | Siyasa | DW | 23.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben shugaban kasar Cote d'Ivoire

A Kasar Cote d'Ivoire an kammala shirye-shiryen zaben chugaban kasa na karszhen mako, domin zaben sabon shugaban kasa tsakanin 'yan takara.

Fiye da mutane milyan shida suka yi rajista inji hukuma zabe mai zaman kanta ta kasar, inda a cikin shirye-shiryen zaben mutane ke fata kan fannin tsaro idan aka dubi zaben da ya wuce na 2010 da ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane dubu-uku.

Ya zuwa yanzu dai za a iya cewa komai ya kammala dangane da duk wasu shirye-shiryen zaben shugaban kasa Cote d'Ivoire. Sai dai kuma a bangare guda mafi yawan masu kada kuri'a na fargabar abin da ka iya biyo baya, idan aka tabbatar da sakamakon zaben, musamman idan suka yi la'akari da yakin basasa da ya barke a kasar shekara ta 2010, duk da cewa a wannan fannin hukumomin kasar tare da hadin gwiwar majalisa dinkin duniya a kasar sun dauki kwararan matakai domin ganin zaben ya kammala cikin nasara.

'Yan kasar da dama ne ke ganin cewa ya kamata Cote d'Ivoire ta shiga sahun kasashen da aka gudanar da ingantaccen zabe a wannan karo. An jibe dubban jami'an tsaro dmoin tabbatar da zaman lafiya da kare lafiya da dukiyoyi mutane.

Sauti da bidiyo akan labarin