1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murnar lashe zabe gabanin bayyana sakamako a Senegal

Abdoulaye Mamane Amadou
February 25, 2019

Wasu 'yan takarar shugaban kasa a Senegal sun soki sanarwar firaministan kasar na bayyna Macky Sall a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da ya gudana a karshen mako

https://p.dw.com/p/3E3bt
Senegal Präsidentschaftswahlen | Macky Sall
Hoto: Imago/Xinhua/D. Gueye

Manyan 'yan adawa a takarar shugaban kasar Senegal, sun soki matakin bangaren gwamnati na ayyna Shugaba Macky Sall a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da ya gudana a ranar Lahadi tun gabannin hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana sanarwar sakamako.

Firaministan Senegal ya yi ikirarin cewa Shugaba Macky Sall ya lashe zaben da aka gudanar a karshen mako, yayin da magoya bayan Shugaba Macky Sall suka fantsama da murna, sakamakon ikrarin firaministan, ko da yake suna murnar ce sao'i kalilan bayan an rufe rumfunoni zaben shugaban kasar, kana tuni wannan ikirari daga bangaren gwamnatin Senegal, ya janyo zazzafar suka daga biyu cikin 'yan takarar jam'iyyun adawa da suka fafata da Shugaba Macky Sall.

Tsohon firaiministan kasar kuma dan takarar shugabancin jam'iyyar PUR Idrissa Seck, ya zargi kafafen yada labarun ketare da yin riga malam masallaci wurin bayyana sakamakon zaben, a yayin da shi kuma daya dan takarar Ousmane Sonko ya zargi Shugaba Marcky Sall da neman murkushe tasirin 'yan hamayya da karfin gwamnati. An dai samu karancin yawan 'yan takaran da suka fito kalubalantar Macky Sall a zaben na darewa kan kujerar shugaban kasa, inda mutane biyar ne kawai ba tare da kuma halartar wasu jiga-jigan jam'iyyun adawa ba. A yanzu dai ana dakon samun kwarya kwaryan sakamakon zaben a hukumance, wanda shi ne kadai ke iya tantance yiwuwar zuwa zagaye na biyu tsakanin 'yan takarar biyar ko a'a, idan daya daga cikinsu ya kasa samun sama da kashi 50 cikin dari na kuri'un da aka kada a zagayen farko.