Zaben sabon shugaba a FIFA | Labarai | DW | 26.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben sabon shugaba a FIFA

Hukumar kwallon kafa ta Amirka ta nuna goyon bayanta ga Alhussein yayin da suka raba gari da Kanada da ke goyon bayan Gianni Infantino.

FIFA Bewerber

Hotunan 'yan takarar kujerar shugabancin FIFA

A ranar Alhamis hukumar kwallon kafa ta Amirka ta bayyana cewa za ta zabi Yarima Ali bin Alhussein dan ya jagoranci hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da ke fama da rikici na shugabanci tun bayan bankado badakalar cin hanci da rashawa a tsakanin tsaffin shugabanninta.

Shugaban hukumar kwallon kafar ta Amirka Sunil Gulati ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter bayan tun da fari ya ce ya yi wata ganawa da 'yan takarar shugabancin na hukumar FIFA guda biyar a yammacin na ranar Alhamis a Zurich.

Ita ma hukumar kwallon kafa ta Kanada da take bayyana tata aniyar kan wannan zabe na ranar Juma'an nan ta ce za ta zabi Gianni Infantino a wannan zabe da za a yi Switzerland dan maye gurbin Sepp Blatter.