1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Switzerland na son dena gwaji kan dabbobi

Abdul-raheem Hassan
February 13, 2022

Idan kuri'ar raba gardama ta yi tasiri, Switzerland za ta zama kasa ta farko da ta haramta gwajin dabbobi. Masu jefa ƙuri'a kuma za su yanke shawara ko za su tsaurara matakan hana tallace-tallacen taba sigari.

https://p.dw.com/p/46wY0
Taba sigari
Hoto: Oleksandr Latkun/Zoonar/picture alliance

Masu kada kuri'a a kasar Switzerland na kada kuri'unsu a zaben raba gardama a yau Lahadin, domin yanke hukunci kan batutuwa da dama da suka hada da hana gwajin dabbobi, da karfafa tallafin kudi ga kafafen yada labarai na cikin gida, da tsaurara matakan dakile shan taba.

An bude rumfunan kada kuri'a na kai tsaye kan batutuwan zaben raba gardama, wadanda ke cikin tsarin dimokuradiyyar kasar kai tsaye, sai dai galibin masu jefa kuri'a a kasar Switzerland, sun riga sun kada kuri'unsu ta hanyar waya.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a na iya yin tasiri sosai a kan manyan masana'antu biyu na kasar - bangaren harhada magunguna da katafaren kamfanin buga sigarin da ke da hedkwata a kasar Switzerland.

Daya daga cikin muhimman matakan da aka dauka kan zaben shi ne ko masu jefa kuri'a za su amince da hana gwajin dabbobi da na mutane za ta kasance kasa ta farko a duniya da ta hana gwajin dabbobi.

Masu fafutukar kare hakkin dabbobi sun tattara isassun sa hannu don sanya tambaya a kan katin zabe. Shirin ya yi kira da a haramta duk wani gwaji kan dabbobi da mutane nan gaba, da kuma hana shigo da duk wani sabon kayayyakin da aka kera sakamakon gwajin dabbobi.